Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Brazil Jair Bolsonaro, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin salwantar rayuka a kasar.
A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce ya kadu matuka da samun labarin mummunar ambaliyar ruwar da ta afku a arewa maso gabashin Brazil, wadda ta haddasa hasarar rayuka da dukiya.
Shugaba Xi ya kuma mika sakon ta’aziyya da ma jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da jama’ar yankunan da bala’in ya shafa.
Ya kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin hanzari.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp