Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga dandalin kirkire-kirkire na Pujiang na shekarar 2023 da aka bude yau Lahadi a birnin Shanghai.
A cikin wasikar tasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, duniya a yau tana fuskantar sauye-sauye cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba a cikin karni, kuma ana samun sabon zagaye na juyin juya hali a fannin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana’antu.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin dabarun bude kofa ga kasashen waje da samun moriyar juna, da ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje, da inganta mu’amalar kimiyya da fasaha ta kasa da kasa, da ma yin hadin gwiwa, da zuciya guda, da fito da karin matakai daban daban, da gina tsarin muhallin takara na kirkire-kirkire na duniya mai adalci maras gurbata muhalli, da yin aiki tare da sauran kasashe, wajen samar da yanayi mai bude kofa, adalci, da rashin nuna wariya ga ci gaban kimiyya da fasaha.
Ana sa ran dandalin kirkire-kirkire na Pujiang, zai kiyaye taken kirkire-kirkire, da zaburar da sabbin dabaru, da yada sabbin tunani, da kara inganta ruhin kirkire-kirkire, da samar da sabbin gudummowa wajen ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha gaba, da inganta rayuwar daukacin bil Adama. (Ibrahim Yaya)