Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet.
A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a matakin koli.
Ya kara da cewa, a yau, bayan shekaru 80 da afkuwar hakan, sakamakon kokarin hadin gwiwa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha na kara habaka tare da sabon kuzari, inda ta zama wani sabon nau’in zumuncin kasa da kasa abin koyi a tsakanin manyan kasashe.
Shugaban na kasar Sin ya kuma bayyana cewa, yana fatan kafofin watsa labaru na kasashen biyu za su hada karfi da karfe don ci gaba da yin aiki tare a bisa manufa guda, da gudanar da kasaitacciyar musayar al’adu da cudanyar jama’a da ke hade zukatan al’umma wuri guda, ta yadda za a kara matsa kaimi ga karfafa fahimtar juna da kauna da zumunci a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da kara inganta cikakkiyar dangantakar Sin da Rasha ta fuskar tsare-tsaren ci gaba a sabon zamani, da bayar da sabbin dimbin gudummawa ga gina al’umma mai makoma guda ga daukacin bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp