Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Yangquan na lardin Shanxi a yau Litinin.
Shugaban ya ziyarci dandalin da aka kebe domin tunawa da katafaren gangamin soji na yaki da harin Japan, inda ya gabatar da furanni ga wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin. Ya kuma ziyarci babban dakin tunawa da gangamin. Shugaban ya kuma yi bitar irin jarumtar da sojojin suka yi yayin yakin da kuma tarihin yadda JKS ta jagoranci sojoji da al’umma wajen hada kai domin yakar ‘yan adawa da bijirewa kutsen Japan, da fahimtar tarihin juyin juya hali a wurin da gado da yayata ruhin yakin kin harin Japan.
Daga baya, ya je wani kamfanin kere-kere na valve dake birnin, inda ya fahimci kokarin da lardin ke yi na inganta sauye-sauye da daukaka darajar masana’antu da samar da ci gaba mai inganci.
Shugaba Xi ya kuma yi rangadi a wuraren kere-kere da nune-nune kayayyaki da ma tattaunawa da ma’aikatan kamfanin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp