Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar wani mai aikin sa kai dake rarraba shara a titin Jiaxing na yankin Hongkou dake birnin Shanghai, inda ya bayyana fatansa na ganin an inganta aikin rarraba shara.
Xi Jinping ya bayyana cikin wasikarsa cewa, rarraba shara da amfani da albarkatu yadda ya kamata, dabara ce mai kyau dake bukatar hada hannu daga dukkan bangarori, wanda kuma ya kamata mazauna birane da kauyuka su shiga a dama da su. Ya ce yana fatan ma’aikacin na sa kai zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin yankin da ma karfafawa karin mazauna gwiwar nuna dabi’a ta kwarai ta rarraba shara.
A shekarun baya-bayan nan, aikin rarraba shara a kasar Sin na kara fadada, inda birane 297 suke aiwatar da tsarin rarraba shara a gidaje, matakin ya shafi kaso 82.5 na unguwanni jama’a. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp