Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin da ya kara kaimi wajen inganta bunkasa tattalin arzikin zirin kogin Yangtze, da gaggauta yin aiki don gina kansa a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da bunkasa yankin tsakiyar kasar, da kuma rubuta nasa babi a sha’anin zamanantar da kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya kai lardin daga ranar Litinin zuwa Laraba. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp