Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasan kasarsa da su zage damtse, wajen bayar da gudummawar cimma nasarar zamanantar da kasa, ta hanyar yin dukkanin sadaukarwa da kasar ke bukata daga gare su.
Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne cikin martanin wasikar da ya aike ga rukunin malamai masu aikin sa kai, a wata makaranta dake yankin kan iyakan kasar mai nisa, karkashin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
 
			




 
							








