Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin bude taro na 25 na majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO, a yau Litinin a birnin tashar ruwa na Tianjin.
Cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya ce SCO ta bunkasa zuwa kungiyar shiyya mafi girma a duniya, wadda ke kunshe da adadin kasashe da suka kai 26, tare da hade sama da yankuna 50, da jimillar kimar tattalin arziki da ta kusa dala tiriliyan 30.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, har kullum SCO na goyon bayan sassan kasa da kasa a fannin tabbatar da gaskiya da adalci, da yin tafiya tare da dukkanin sassa, da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai, tana kuma adawa da danniya da siyasar nuna fin karfi, don haka ta zama ginshikin wanzar da zaman lafiya a duniya. A hannu guda kuma darajar jimillar hada-hadar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashe membobin SCO ta kai dala tiriliyan 2.3, adadin da ya dara wanda aka yi hasashe tun kafin cikar wa’adin.
Har ila yau, shugaba Xi ya ce cikin wannan shekara, Sin za ta samar da tallafin yuan biliyan biyu, kimanin dalar Amurka miliyan 280.5 ga kasashe membobin SCO. Kazalika, za ta samar da rancen yuan biliyan 10, kimanin dalar Amurka biliyan 1.4 ga tsarin hada-hadar bankunan kasashe membobin kungiyar cikin shekaru uku dake tafe. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp