An gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ko APEC a takaice a San Francisco na Amurka a jiya Jummaa bisa agogon Amurka.
A cikin shekaru 30 da suka gabata, abubuwan ban alajabi da mambobi 21 na kungiyar APEC suka kafa tare sun jawo hankalin kasa da kasa. A nan gaba kuma, yaya yankin Asiya da Pasifik zai cimma “shekaru 30 na ci gaba”? Shugaban Sin Xi Jinping ya ba da amsa a cikin jawabinsa, kuma abu mafi muhimmanci a ciki shi ne tsayawa tsayin daka kan bude kofa da hadin gwiwa da kuma samun ci gaba tare.
- Ganawar San Francisco: Tsaraba Daga Jawabin Shugaba Xi Kan Bukatar Sin Da Amurka Su Nuna Su Manya Ne A Aikace
- An Kafa Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje 41,947 A Kasar Sin Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
Ya kuma gabatar da shawarwari guda 4 a cikin jawabinsa, wato tsayawa tsayin daka kan samun bunkasuwa ta hanyar kirkire-kirkire, da nacewa kan bude kofa ga kasashen waje, da tsayawa tsayin daka kan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tsayawa tsayin daka kan kawo alheri ga dukkan alummun kasashen duniya. Kuma abu mafi muhimmanci a cikinsu shi ne tsayawa tsayin daka kan raayin bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa da kuma samun ci gaba tare. Wannan raayi shi ne tushen shirin Xi Jinping, kuma shi ne ruhin tarihin ci gaban yankin Asiya da Pacific a cikin shekaru 30 da suka gabata.
“Bude kofa yana haifar da wadata, yayin da rufe kofa ke haifar da koma baya.” Xi Jinping ya sha bayyana cewa, wannan ita ce muhimmiyar kwarewar da ta taimakawa Sin da ma duniya wajen samun ci gaba. Tarihin wadatar yankin Asiya da Pacific ya kuma shaida cewa, rashin hadin kai babban hadari ne. (Safiyah Ma)