A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarkin Cambodia Norodom Sihamoni. Bayan haka ya karbi lambar yabo ta ‘yancin kasa ta masarautar Cambodia daga sarki Sihamoni, a fadar sarauta ta Phnom Penh.
Xi ya kuma gana da shugaban jam’iyyar jama’ar Cambodia kuma shugaban majalisar dattawan kasar Samdech Techo Hun Sen, da kuma firaminstan Cambodia Hun Manet.
Xi ya isa Cambodia ne a safiyar ranar Alhamis don ziyarar aiki. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp