Da yammacin ranar 16 ga Nuwamba agogon kasar Peru, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden a birnin Lima, fadar mulkin kasar Peru.
Yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru hudu da suka gabata, duk da cewa huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da matsala, amma sassan biyu bisa tattaunawa tare da hadin gwiwa tsakaninsu, ana iya cewa, ana gudanar da hulda lami lafiya. Huldar Sin da Amurka ta shaida fasahohin da aka samu bayan da suka daddale huldar difilomasiyya shekaru 45 da suka gabata. Idan kasashen biyu suka mayar da juna abokai, huldarsu za ta ci gaba cikin sauri. Amma idan suka mayar da juna abokan gaba, har suka lahanta moriyar juna, to huldar za ta gamu da matsala, ko kuma za ta samu koma-baya.
Xi ya kara da cewa, an yi babban zabe a Amurka kwanan baya. Kasar Sin tana son ci gaba da tattaunawar hadin gwiwa da gwamnatin kasar Amurka domin kyautata huldar sassan biyu, tare da haifar da alfanu ga al’ummun kasashen biyu. (Mai fassara: Jamila)