Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin tawagogin kasa da kasa dake halartar taron kwamitin ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO.
Yayin ganawar tasu, Xi ya nanata cewa, ya kamata SCO ta bi hanyar da ta dace da karawa kanta kwarin gwiwa da daukar matakan da suka dace, don baiwa duk fadin duniya tabbaci da ingantaccen karfi, duk da cewa ana fuskantar yanayi masu sarkakiya a duniya.
Xi ya kuma ba da shawarwari 3, na farko rike akidar ruhin SCO. Na biyu kuma biyan bukatun jama’a ta hanyar daukar matakai masu yakini na zurfafa hadin gwiwarsu. Na uku kuwa, sauke nauyin dake wuyansu a wannan zamani da muke ciki, ta yadda za a samu kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya a duniya.
Ban da wannan kuma, Xi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov. (Amina Xu)