Da daren yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude gasar wasanni ta Asiya karo 19, tare da ayyana bude gasar. Bikin bude gasar ya gudana ne a birnin Hangzhou, fadar mulkin lardin Zhejiang na kasar.
Bugu da kari, a yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan sun shiryawa manyan baki mahalarta bikin bude gasar wasanni ta Asiya karo na 19 liyafar girmamawa a birnin Hangzhou inda za a gudanar da babbar gasar.
- Xi Jinping Ya Bukaci A Raya Masana’antu Masu Inganci
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kwamitin Olympics Da Wasu Shugabannin Kasashen Duniya
Cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya yi maraba da daukacin baki mahalarta gasar, yana mai cewa, Sin za ta cika alkawarin da ta yi, tare da tabbatar da nasarar gasar ta wannan karo, kana za ta gudanar da gasa mai halayyar musamman ta Sin, da salon nahiyar Asiya, kuma mai matukar kayatarwa.
Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada burin kasarsa na ingiza dunkulewar sassa daban daban ta hanyar wasanni, da bunkasa kwarin gwiwa ga wayewar kan al’ummun Asiya, da yayata cudanya, da koyi da juna, tare da karfafa samar da sabbin nasarori ga wayewar kan nahiyar Asiya.
Sannan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarkin masarautar Kambodiya Norodom Sihamoni, da firaministan Timor-Leste Xanana Gusmao, da firaministan Koriya ta kudu Han Duck-soo, da na kasar Nepal Pushpa Kamal Dahal Prachanda, wadanda suka halarci bikin bude gasar wasannin Asiya karo na 19 yau Asabar a birnin Hangzhou. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)