Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi kira da a zage damtse, wajen bunkasa tattalin arzikin kogin Yangtze mai inganci, domin samun goyon baya da cimma burin zamanantar da kasar Sin.
Xi, wanda har ila shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana haka ne, a ranar 12 ga wata a yayin wani taron tattaunawa da ya jagoranta kan raya ci gaban tattalin arzikin kogin Yangtze.
- Tanadin Kudin Kasar Sin Ya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da ‘Yanci Da Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa Da Inganta Rayuwar Jama’a A Afirka
- Zhang Jun: Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Rawar Gani Wajen Cimma Burin Bunkasa Afirka Cikin Lumana
Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya yi rangadi a biranen Jingdezhen, da Shangrao na lardin Jiangxi dake gabashin kasar Sin.
Xi Jinping, wanda ya ziyarci biranen a ranar 11 ga wata, ya ganewa idanun sa wani rukunin gine ginen al’adun gargajiya masu tsohon tarihi, da kamfanin AVIC Changhe na kera jiragen sama dake birnin Jingdezhen. Kaza lika ya ziyarci wani kauye dake karkashin gundumar Wuyuan na birnin Shangrao.
Yayin wannan ziyara, ya kuma nazarci matakan da ake aiwatarwa na kariya, da gadon al’adun sarrafa kayan fadi-ka-mutu, da fasahohin kere-kere, da aikin kare muhallin halittun fadamu, da kuma raya kauyuka.(Kande Gao)