Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a kara tabbatar da amfani da filaye, don samun bunkasuwa mai inganci a yankunan da ke da karfin yin takara, kana ya kamata a kara inganta ayyukan ba da agajin gaggawa daga tushe.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taro na hudu na kwamitin kula da ayyukan zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni na kwamitin kolin JKS karo na 20. (Ibrahim)