Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara aiwatar da dabarun kara karfin sojojin kasar, ta hanyar horar da kwararrun sojoji a sabon zamani.
Yayin da yake jagoranta tare da gabatar da jawabi a taron nazari na rukunin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS da ya gudana jiya Alhamis, Xi Jinping ya kuma bukaci da a yi kokarin ba da gudummawar da ta dace ga rawar da masu hazaka ke takawa wajen jagoranci da tabbatar da gina rundunar soja mai karfi.(Ibrahim)
Talla