Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar kasar ta zama babbar kasa a fannin ilmi, a gabar da shugabannin jam’iyyar suka gudanar da wani zaman nazari jiya Litinin.
Da yake jagorantar taron nazarin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi ya ce, manufar ta kasance wata muhimmiyar madogara ta gina babbar kasa mai ra’ayin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni, wanda ke zama wani muhimmin goyon baya ga samun dogaro da kai da karfi a fannin kimiyya, da fasaha, da kuma ingantacciyar hanyar inganta wadata ga kowa.
Don haka Xi ya yi kira da a gaggauta sabunta fannin ilmi, domin ba da goyon baya mai karfi don ciyar da kasar Sin gaba ta fuskar farfado da daukacin Sinawa daga dukkan fannoni. (Mai fassarawa: Ibrahim)