Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar samar da sabon tsarin tattalin arziki mai kara bude kofa, a matsayin muhimmiyar dabarar inganta gyare-gyare da samun ci gaba ta hanyar bude kofa, yana mai cewa ya kamata a kuma samar da wani sabon tsarin neman ci gaba a bangaren bayar da hidimomi da mayar da hankali kan bude kofa.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a yau, yayin da ya jagoranci taro na biyu na hukumar tsakiya mai kula da zurfafa gyare-gyare a gida ta JKS.
Ya kara da cewa, ya kamata a mayar da hankali kan yin gyare-gyare ta fannonin zuba jari da cinikayya da harkokin kudi da kirkire-kirkire da sauran muhimman bangarorin musaya da hadin gwiwa da kasashen waje, da inganta matakai da manufofi da za su taimakawa hakan da kuma daukaka manufar bude kofa ta kasar Sin ga duniya, zuwa wani sabon mataki. (Fa’iza)