Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin aiwatar da muhimman manufofi, da bude sabbin babuka, tare da daukar managartan matakai, wadanda za su ba da damar bude sabon babin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, a sabon tafarki da kasar sa ta sa gaba.
Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a jiya Juma’a, yayin da yake jagorantar taron farko na hukumar aiwatar da zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a dukkanin fannoni, karkashin kwamitin koli na 20 na JKS.
Ya ce domin cimma manufofi, da ayyukan da aka sanya a gaba a sabon tafarki na sabon zamani, ya zama wajibi a dauki ayyukan zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a dukkanin fannoni a matsayin jigon ingiza zamanantarwa irin ta kasar Sin, kana hakan ya zamo wani fifiko na daidaita dukkanin yanayi, wanda zai shawo kan dukkanin sauye-sauye da ka iya bijirowa, a kuma samar da sabon ci gaba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp