Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron shugabannin JKS a yau Alhamis, domin nazari, da tsara ayyukan jin kai, biyowa bayan girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a jihar Xizang mai cin gashin kai a farkon makon nan.
Taron na zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya jaddada cewa, har yanzu aikin ba da tallafin jin kai na cikin wani muhimmin lokaci, kuma dole ne a kara azamar aikin ba tare da sassautawa ba. Taron ya kuma bayyana bukatar tabbatar da nasarar shawo kan wannan ibtila’i mai tsananin gaske. (Saminu Alhassan)