A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron tattaunawar sabuwar huldar kasa da kasa kan nazarin sararin samaniya da aikin kirkire-kirkire tsakanin MDD da Sin.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuna cewa, a shekarun baya-baya nan, Sin ta himmantu wajen gudanar da ayyukan nazarin sararin samaniya, wadanda suka taimaka wajen habaka ilmin Bil Adama kan sararin samaniya, da kara kawo alheri ga daukacin Bil Adama baki daya. Aikin binciken sararin samaniya ba ya karewa.
Kasar Sin na fatan kara hada kai da kasa da kasa da habaka mu’ammala da hadin gwiwa, da yin nazari kan sirrikan sararin samaniya tare, da amfani da sararin samaniya cikin lumana, da ingiza bunkasuwar kimiyya da fasahar da za ta amfani al’ummar duniya.
An bude wannan taro ne a birnin Haikou na lardin Hainan. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp