Yau Labara, an gudanar da taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “Ziri daya da hanya daya” BRF karo na uku a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana shugaban kasar, shugaban rundunar sojin kasar kasar Sin, Xi Jinping ya halarci bikin bude taron, tare da gabatar da jawabi.
A yayin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da sanarwar ayyuka 8 da kasar Sin za ta gudanar don tallafawa hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” wato BRI mai inganci, ciki har da shimfida hanyar sadarwa mai alaka da hadin gwiwa mai bangarori uku na shawarar “ziri daya da hanya daya”, da goyon bayan raya tattalin arzikin duniya mai bin salon bude kofa, da aiwatar da hadin gwiwa mai inganci, da inganta samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta kimiyya da fasaha, da inganta mu’amala tsakanin jama’a, da raya hanya ba tare da cin hanci da rashawa, da kuma inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Haka kuma, Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 10 da suka gabata, mun tsaya tsayin daka da yin hadin gwiwa domin inganta shawarar “Ziri daya da hanya daya”, wato BRI a takaice, inda hadin gwiwar dake tsakanin kasashen da abin ya shafa, ya bunkasa cikin sauri, har aka kai ga cimma dimbin sakamako masu gamsarwa.
Ya ce, cikin wadannan shekaru 10 ke nan, mun habaka hadin gwiwar kasashen duniya ta hanyoyin kasa, da na teku, da na sama, da ma hanyoyin sadarwa. Matakan da suka taka muhimmiya rawa wajen karfafa mu’amalar hajoji, da kudade, da fasahohi, da masana a tsakanin kasashen duniya, lamarin da ya kai ga bude sabon babin habaka hanyar siliki a sabon zamani.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, ana mai da hankali kan hadin gwiwa wajen habaka shawarar “ziri daya da hanya daya”, domin hadin gwiwa da taimakawa juna muhimman hanyoyi ne na samun dauwamammen ci gaba na shawarar. Muna son kafa dangantakar cude-ni-in-cude-ka, da aiwatar da ka’idojin yin mu’amala da juna da cimma moriyar juna, ta yadda za a samu ci gaba tare, da cimma nasarori cikin hadin gwiwa.
Bugu da kari, ya ce, ba za mu nuna adawa kan bambancin al’adu ba, kuma, ba za mu yi gasar siyasa bisa yankunan da muke ciki ba, balle ma yakin siyasa a tsakanin kawance daban daban. Kasar Sin tana adawa da takunkumin rashin adalci, da kalubalen tattalin arziki, kuma ba ta son dakile huldar ciniki dake tsakaninta da sauran kasashen duniya.
Ya kara da cewa, mun gane cewa, dukkanin bil Adama na da makomar bai daya, idan babu bunkasuwar kasashen duniya, ba za a sami bunkasuwar kasar Sin ba, kana, idan kasar Sin ta bunkasa kamar yadda ake fata, tabbas kasashen duniya za su sami karin bunkasuwa.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, wadannan shekaru 10 da suka gabata sun nuna mana cewa, inganta shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, ya kasance abu mafi dacewa da muka yi, ya kuma dace da halin da muke ciki. Ya kamata mu sauke nauyin da ke kanmu yadda ya kamata domin kare tarihin bil Adama, da kiyaye al’umma, tare da raya duniyarmu, haka kuma, ya dace mu hada kanmu wajen fuskantar kalubalolin dake gabanmu, ta yadda za a samar da wata makoma mai haske ga ’ya’yanmu da jikokinmu. (Mai Fassarawa: Safiyah Ma&Maryam Yang)