Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasar sa za ta kara bude kofofin ta a fannonin ba da hidimomi, wadanda suka hada da na fasahar sadarwar wayar tarho, da yawon bude ido, da jarrabawa a bangarorin shari’a da ilimin koyar da sana’o’i.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin da yake jawabi ta kafar bidiyo ga taron baje kolin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023, game da hada hadar cinikayyar ba da hidima ko CIFTIS.
Xi ya ce domin bunkasa damar ci gaba a fannin kara bude kofofin kasar Sin, ta yadda kowa zai iya shiga a dama da shi, Sin za ta fadada damammakin kasa da kasa na inganta yankunan cinikayya maras shinge, za ta kuma shiga a dama da ita wajen gudanar da shawarwarin shawo kan mummunan tasirin dake akwai, don gane da sassan ba da hidima da na zuba jari da ake kayyadewa.
Kaza lika, shugaban na Sin ya ce babban hadadden yankin gwaji domin bude kofa a fannonin ba da hidima na Sin, da yankunan cinikayya maras shinge na gwaji, da tashoshin ruwa na gudanar da cinikayya maras shinge, su ne za su fara daidaita manufofin su, ta yadda za su yi kafada da kafada da managartan dokokin raya tattalin arziki, da cinikayya na kasa da kasa.
Bikin baje kolin na bana dai na da taken “Bude kofa na haifar da ci gaba, yin hadin gwiwa na inganta makoma”. Zai kuma gudana tsakanin Asabar din nan zuwa ranar Larabar makon gobe. Kaza lika yayin baje kolin na wannan lokaci za a gudanar da sama da ayyuka 200, ciki har da dandaloli, da shawarwari, da tarukan karawa juna sani.
Bikin na bana ya samu halartar kasashe, da hukumomin kasa da kasa 83, yayin da kuma manyan kamfanoni da cibiyoyi sama da 70 ke baje nasarorin su, kana akwai sama da kamfanoni 2,400 dake halartar baje kolin a zahiri. (Mai fassara: Saminu Alhassan)