Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata, ya aike da sako ga Duma Boko domin taya shi murnar cin zabe da ya yi a matsayin shugaban kasar Botswana.
A cikin sakon nasa, Xi ya bayyana cewa, Sin da Botswana suna da dadadden zumunci, yana mai cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba mai inganci, tare da samun nasarori masu ban mamaki a hadin gwiwarsu a fannonin samar da ababen more rayuwa, da makamashi mai tsafta, da kuma da lafiyar jama’a.
Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci ga raya dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Botswana, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Boko don daga dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu zuwa wani matsayi mai girma, da samar da karin moriya ga jama’ar kasashen biyu. (Yahaya)