Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Felix Antoine Tshisekedi murna ta wayar tarho, bisa lashe zaben shugaban kasar Jamhuriyyar dimokuradiyya ta Congo.
Xi Jinping ya ce, kasar Congo Kinshasa abokiyar arziki ce ta kasar Sin, kuma abokiyar hadin gwiwarta bisa manyan tsare-tsare. A cewarsa, cikin ’yan shekarun nan, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na bunkasuwa cikin sauri, inda suka cimma sakamako da dama, da zurfafa daddaden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Shugaba Xi yana kuma fatan hada gwiwa da shugaba Tshisekedi wajen karfafa fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu, ta yadda za a habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen zuwa wani sabon matsayi. (Mai Fassara: Maryam Yang)