Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murna ga malamai, dalibai, da tsofaffin daliban Jami’ar koyon fasahar tsaro ta kasar Sin, yayin da jami’ar ke cika shekaru 70 da kafuwa.
A Jumma’ar nan ce, Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar kolin sojan kasar, ya aike da wasikar taya murna ga jami’ar.
Bisa wani labari daban da aka bayar, an ce, a gobe Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da jawabi ta bidiyo, yayin bikin kaddamar da baje kolin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023, wanda ya shafi hada hadar cinikayyar ba da hidimomi, ko CIFTIS a takaice.
Shugaban na Sin zai gabatar da jawabin ne a nan birnin Beijing, kuma kafofin CMG da http://news.cn/ na Xinhuanet za su watsa jawabin nasa kai tsaye. (Mai fassara: Ibrahim, Saminu Alhassan)