A ranar Talata ne Shugaba Xi jinping na kasar Sin ya ba da amsar wasikar John Easterbrook, jikan Joseph Stilwell, tsohon janar na kasar Amurka, wanda ya taimakawa Sinawa a yakin da kasar Sin ta yi na adawa da hare-haren da sojin Japan suka kai wa kasar Sin a lokacin yakin duniya na biyu.
A cikin wasikar, Xi ya mika godiyarsa ga Easterbrook saboda yada labaran mu’amalar sada zumunci da Stilwell da iyalansa suka yi da kasar Sin tsawon zamani da dama.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, a kwanan baya an gudanar da bukukuwan cika shekaru 140 na ranar haihuwar Joseph Stilwell, a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin. Ya ce ya yi farin cikin ganin yadda yanayin abota tsakanin Sin da Amurka ta ci gaba da wanzuwa a cikin danginsa har zuwa zamani na biyar. (Yahaya)