Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Javier Milei murnar lashe zaben shugaban kasar Argentina.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau.
- Bunkasuwar Sin Na Taka Rawa Ga Farfadowar Yankin Asiya Da Pacific
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila
Mao Ning ta ce, cikin sakonsa na taya murna, Xi Jinping ya ce, Sin da Argentina, dukkansu manyan kasashe ne masu tasowa da tattalin arzikinsu ke samun ci gaba, kuma suna bin ka’idar mutunta juna da daidaito da moriyar juna. Haka kuma suna goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muradun juna.
Da yake bayyana hadin gwiwarsu a bangarori da dama a matsayin wanda ya samar da alfanu ga al’ummomin kasashen biyu, Xi Jinping ya ce, abotar dake tsakanin Sin da Argentina ta darsu a zukatan al’ummominsu kuma ta zama wata matsaya da al’ummomin nasu suka cimma a dukkan bangarorin rayuwa, domin inganta raya huldar kasashen biyu.
Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da sabuwar gwamnatin Argentina wajen ci gaba da dadaddiyar abotar, da fadada hadin gwiwar moriyar juna da daukaka huldar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannonin dake tsakaninsu, domin al’ummominsu su amfana. (Fa’iza Mustapha)