Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a hada karfi da karfe don nema da kuma kiyaye zaman lafiya.
A cikin muhimmin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, yayin bikin bude dandalin kasuwanci na BRICS, shugaba Xi ya bayyana cewa, tarihi ya nuna cewa mulkin kama karya, siyasar rukuni da kuma fadace-fadacen kungiyanci, ba sa kawo zaman lafiya ko kwanciyar hankali sai dai yaki da rikici.
Xi ya kara da cewa, wadanda suka sanya siyasa, da amfani da makamai, da kuma sanya takunkumi da gangan ta hanyar cin gajiyar karfin tsarin harkoki da hada-hadar kudi na kasa da kasa, daga karshe za su cutar da wasu da ma kansu, tare da haifar da bala’i ga daukacin al’ummar duniya. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)