Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yau Talata a birnin Pretoria cewa, yana son yin aiki tare da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wajen ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka ta Kudu zuwa wani sabon mataki.
A wani sabon mafari na tarihi, shugaba Xi ya bayyana cewa, kara sada zumunta, da zurfafa alaka da hadin gwiwa, sun kasance burin kasashen biyu, da kuma aikin da zamani ya dora musu.
Xi ya bayyana hakan ne, a yayin wata ganawa da Ramaphosa bayan isarsa Afirka ta Kudu jiya Litinin, inda zai halarci taron koli na kasashen BRICS karo na 15, kana shi da Ramaphosa za su jagoranci taron tattaunawa na shugabannin kasashen Sin da Afirka. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp