Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azamar yayata Babbar Ganuwar kasar Sin, ta yadda karin mutane za su san ta, kana a kara adadin mutanen dake shiga ayyukan kare ganuwar, ta yadda za a mika gadonta zuwa zuri’o’i na gaba.
Shugaba Xi ya yi tsokacin ne cikin wasikar martani da ya aike ga mazauna kauyen dake kusa da yankin Badaling na Babbar Ganuwar dake arewacin wajen birnin Beijing a jiya Talata. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp