Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci jami’an kasar su kara kaimi wajen daukar matakai na gaggawa, da tabbatar da samar wa jama’a dumi da kwanciyar hankali a lokacin sanyi.
Ya kuma bukaci yankin Guangxi mai cin gashin kansa na kabilar Zhuang, da ya mayar da hankali, da yin kirkire-kirkire, da inganta tattalin arzikin teku, da kara bude kofa ga kasashen waje, da samun bunkasuwa, da rubuta wani babi na ciyar da aikin zamanantar da kasar Sin gaba, yayin rangadin da ya kai yankin da ke kudancin kasar Sin daga ranar jiya Alhamis zuwa yau Jumma’a.(Ibrahim)
Talla