Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da hanzarta fadada tsarin BRICS, da kara kokarin tabbatar da tafiyar da harkokin duniya bisa adalci.
Xi ya bayyana hakan ne, Larabar nan a yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kolin kasashen BRICS karo na 15. Ya kuma bayyana cewa, ci gaba wani hakki ne da ba a za a iya tauyewa dukkan kasashe ba, kuma ba wata dama ce ta wasu kasashe kalilan ba. Ya kamata kowa ya rubuta kuma ya kiyaye ka’idojin kasa da kasa kamar yadda kundin tsarin MDD ya tanada, kuma ba za a lamunci sanya dokokin cikin gida a matsayin ka’idojin kasa da kasa ba.
Ban da haka kuma, shugaba Xi ya ce, kasar Sin za ta kafa wani rukunin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire na Sin da BRICS na sabon zamani, yayin da kasashen BRICS suka amince da kaddamar da rukunin nazarin fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI) da fadada hadin gwiwar fasahar ta AI.
Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da manufar nan ta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukanin bil adama a zahiri. Shugaban ya yi wannan kira ne a jiya Talata a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, cikin jawabinsa, da ministan ma’aikatar cinikayyar kasar Sin Wang Wentao ya karanta, yayin zaman dandalin kasuwanci na taron BRICS dake gudana yanzu haka.
A cikin jawabin mai taken “Inganta goyon baya da hadin gwiwa domin shawo kan hadurra da kalubale, da hada karfi wajen gina duniya mai karko”, shugaban na Sin ya ce “Ya kamata mu ingiza ci gaba da walwalar kowa da kowa. Akwai bukatar cimma yanayin tsaron duniya na bai daya, da kara zage damtse wajen yin musaya tsakanin mabanbantan wayewar kai, da yin koyi da juna”. Kaza lika shugaba Xi ya ce yunkurowar kasashe masu saurin bunkasar tattalin arziki, da kasashe masu tasowa, wanda kungiyar BRICS ke wakilta, ya yi matukar sauya alkiblar duniya, kuma duk wata turjiya da za a iya fuskanta, ba za ta hana BRICS mai karfi da inganci ci gaba da bunkasa ba.
Har ila yau, Xi ya ce Sin na neman bunkasuwa ta bai daya tare da sauran kasashe masu tasowa, tana kuma martaba moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, kana tana aiki tukuru wajen kara fadada wakilci, da karfin muryar kasashe masu saurin bunkasar tattalin arziki, da takwarorin su kasashe masu tasowa a harkokin kasa da kasa.
Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da zama muhimmiyar dama ga ci gaban duniya. A hannu guda kuma, za ta tsaya tsayin daka wajen ingiza matakan bude kofofin ta, da goyon bayan barin kasuwa ta yi halin ta bisa kyakkyawan yanayi, wanda ya yi daidai da tsarin dokoki na adalci, da kuma gina cudanyar yankunan kasuwanci maras shinge tsakanin kasa da kasa, wanda dukkanin sassa za su amincewa. (Masu Fassara: Saminu Hassan, Ibrahim Yaya)