A Litinin din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa kasarsa ta shirya tsaf wajen yin aiki tare da dukkan bangarori don gina wata sabuwar duniya mai ci gaba ta bai daya bisa adalci.
A yayin da yake jawabi ga zaman farko na taron kolin kungiyar G20 a game da yaki da yunwa da fatara, Xi ya ce “ya kamata a samar da karin gadoji na hadin gwiwa da mayar da nesa ta zamo kusa da rage dogayen shingaye, domin a samu karin kasashe masu tasowa da za su samu ci gaba da cimma nasarar zamanantarwa.”
- Kamata Ya Yi Sin Da Amurka Su Mai Da Hankalinsu A Kan Ci Gaban Duniya
- Shugabannin Sin Da Faransa Sun Rubuta Bayanai Domin Wani Bikin Baje Koli Na Musamman
Domin gina irin wannan duniya da ake fatan gani, Xi ya yi kiran “samar da budadden muhalli da ya hade kowa mai kunshe da rashin nuna wariya domin hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen duniya, irin wanda zai zamo mai alfanu na bai daya da cikakkiyar dunkulewar tattalin arzikin duniya, kana da tallafa wa kasashe masu tasowa wurin kyakkyawar shiga a dama da su a bangaren ci gaban zamani mai fikira da kuma inganta lafiyar muhalli don cike gibin da ke tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu hannu da shuni.
Bugu da kari, Xi ya ce a ko yaushe kasar Sin za ta ci gaba da zama ’yar gida a wurin kasashe masu tasowa kuma abokiyar kawance na tsawon lokaci da za a dogara da ita sannan wacce take fada da cikawa da kara yaukaka zumuncin aiki domin ciyar da kasashe masu tasowa gaba.
Har ila yau, shugaba Xi Jinping ya zayyano matakai guda takwas da kasar Sin ta dauka domin ci gaban duniya a cikin jawabin nasa, ciki har da inganta hadin gwiwar Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, aiwatar da tsare-tsaren ci gaban duniya, tallafa wa bunkasa Afirka, ba da taimako ga hadin gwiwar kasashen duniya a kan rage fatara da samar da wadatar abinci da sauransu.
An dai kaddamar da kawancen kasashen duniya domin yaki da yunwa da fatara ne a zaman farko na taron kolin da ake yi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)