Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi yau Juma’a a birnin Shijiazhuang, babban birnin lardin Hebei na arewacin kasar Sin.
Yayin rangadin, ya ziyarci cibiyar bincike ta kamfanin laturoni ta kasar Sin, da dakin nune-nunen shirin bunkasa yankin masana’antun samar da magunguna da kayayyakin aikin likita, inda ya ga yadda ake bincike da tsare-tsare da samar da kayayyaki da ma kokarin da ake a yankin wajen bunkasa masana’antar. (Fa’iza)