Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jaddada a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin na kalubalantar kungiyar G7 da ta daina nuna bambanci tsakanin kasashe, da taimakawa wajen matsa musu lamba a fannin tattalin arziki.
An ce, kasashe membobin kungiyar G7 za su sanar da tinkarar batun matsin lamba a fannin tattalin arziki, domin aikewa kasar Sin sako. Game da wannan, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, kasar Sin da kanta ta yi fama da matsin lamba a fannin tattalin arziki daga Amurka, kuma ta kasance mai adawa da wannan batu.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya yi bayani game da rahoton kungiyar masanan nahiyar Turai da ya yabawa shawarar ziri daya da hanya daya, inda ya bayyana cewa, duk jita-jitar da ake yadawa game da shawarar ziri daya da hanya daya, da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu bin shawarar, ba su da tushe balle makama.(Zainab)