A ranar 15 ga watan nan na Disamba ne gwamnatin Amurka, ta kara wasu kamfanonin kasar Sin su 36, cikin jerin kamfanonin da ta sanyawa takunkumin shigar da hajojin su cikin Amurka, ciki har da kamfanin Tiandy Technologies, wanda Amurkan ta zarga da aikata danniya, da taimakawa wajen tsare mutane, da leken sirrikan mutane ta amfani da fasahohin zamani, da keta hakkokin bil Adama, matakin da Amurka ta ce wai, ya shafi al’ummun Uygurs, da na Kazakhs, da sauran musulmin kananan kabilun dake sassan kasar ta Sin.
Kamfanin Tiandy Technologies mai hedkwata a birnin Tianjin, na samar da na’urorin sanya ido ne, yana kuma bayar da hidimomi masu nasaba da hakan. Yana kuma hada sassan fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adama da fasahar tattara manyan bayanai, da fasahar ajiyar su, da sauran fasahohin yanar gizo, da na kyamarori, wajen samar da bayanai na tabbatar da tsaro.
Da yake tsokaci kan matakin gwamnatin Amurka kan wannan kamfani, kakakin gwamnatin jihar Xinjiang Xu Guixiang, ya ce kamfanin Tiandy Technologies yana da rajista bisa doka, kuma jihar Xinjiang na amfani da na’urorin sa ne wajen tattara bayanai, da inganta ayyukan jagorancin jihar, da gina al’umma mai yanayin zaman lafiya, ta yadda kowa zai rayu tare da gudanar da ayyuka cikin zaman lafiya da wadatuwa. Xu ya kara da cewa, kamfanin ba ya harin wasu rukunin kabilu ko gungun al’umma, kana ba shi da wani tarihi na keta hakkokin bil Adama, ta hanyar leken asiri ta amfani da manyan fasahohi.
Har ila yau, jami’in ya ce abu ne sananne a duniya, kasashe daban daban na amfani da na’urorin fasahohin zamani, a ayyukan jagorancin al’umma, kuma Amurka ita kan ta na kan gaba, wajen zuba jari, da bincike, da samar da hajoji da manhajoji na inganta tsaro, da tattara manyan bayanai, da samar da dandaloli na killace bayanai.
Don haka, abun tambaya a nan a cewar jami’in shi ne, shi ma wannan mataki na Amurka, na leken asirin Amurkawa ne? (Saminu Alhassan)