Bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar yankin Xizang mai cin gashin kansa na kasar Sin, lamarin da ya zama ba wai kawai lokacin biki ba ne, har ma da waiwaye adon tafiya kan wata turba ta ruhin samun ci gaba da sauye-sauye a yankin kudu maso yammacin kasar Sin. Xizang ya taba kasancewa wani yanki mai nisa dake cikin mawuyacin hali, amma a yanzu ya zama shaida kuma abin kwatance a bangaren juriya, da samun bunkasa da kuma farfado da raya al’adu.
A shekarar 1965, saboda yanayin muhallin yankin Xizang da rashin ababen more rayuwa da suka sada shi da sauran sassan kasar Sin, ya zama yanki mafi girma mai wahalar zuwa a duk fadin kasar. Hanyoyi sun yi karanci, kana mutanen yankin suna rayuwa ba tare da walwala ta a-zo-a-gani ba. Amma zuwa shekarar 2024, yankin ya samu lafiyayyun hanyoyi masu nisan kilomita 124,900, inda aka sada kauyuka da birane da juna. Layin dogo na Qinghai zuwa Xizang da zirga-zirgar jiragen sama 180 da ake yi sun mayar da yankin dake kan tudu mai tsawo da ya zama tamkar saniyar ware zuwa cibiyar hada-hada da samun damammaki.
- Xi: Wajibi Ne A Aiwatar Da Dabarun JKS Wajen Mulkin Yankin Xizang Na Sin A Sabon Zamani
- EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025
Bari mu dauki Kauyen Galai dake Nyingchi na Xizang domin buga misali a kan bunkasar tattalin arzikin yankin. A lokutan baya, kauyen ya dogara ne da noma na ciyar da iyali kawai, amma a yanzu ya shahara ta fuskar yawon bude ido da kuma kafuwar masana’antun inganta muhalli. Tattalin arzikin furen “peach,” wanda ake samu daga bishiyoyin kauyen masu dadadden tarihi da kyawawan wurare masu dausayi, sun zama wani tambari na farfadowar yankin karkara a duniya. Kudin shiga da aka kiyasta samu ga kowane mutum a Galai duk shekara ya zarce yuan 40,000 a shekarar 2024. Yanzu haka mazauna kauyen suna samun kudin shiga ta hanyoyi daban-daban, tun daga kan jigilar kayayyaki, hidimomin baki, da kuma hada-hadar gamayyar kungiyoyin yawon shakatawa.
Karfin tattalin arzikin yankin Xizang ya kai adadin kudin kasar Sin yuan biliyan 276.5 a shekarar 2024, wanda ya ninka sau 155 a kan na shekarar 1965, inda aka rika samun matsakaicin karuwarsa a mizanin shekara-shekara da kaso 8.9%, kana a bana da yankin ke cika shekaru 60 da kafuwa, ana sa ran karfin tattalin arzikin nasa zai haura yuan biliyan 300. Xizang ya samu wannan tagomashin ne daga sassan masana’antun makamashi mai tsafta, da aikin noma, da yawon bude ido a bangaren tarihi da al’adu, bisa goyon bayan kawancensa da wasu lardunan da suka ci gaba a karkashin tsarin ba da tallafi na kasar Sin.
Kazalika, Xizang ya samu ci gaban walwalar jama’a mai zurfi ta yadda mazaunansa ke more rayuwa irin na dan’adam mai ’yanci. An fadada samar da ingantattun harkokin kiwon lafiya da ilimi. An bude manyan tituna zuwa kananan gundumomi da ba a iya kaiwa a baya inda hakan ya kara kawo sauyi ga kula da ayyukan jama’a. Akwai makarantu, da asibitoci, da cibiyoyin koyar da sana’o’i a yankin na zamani, wanda hakan ya bai wa al’ummar Xizang ta yanzu damar yin amfani da kayan aikin da za su kara musu fahimtar albarkatun da suke da su.
A halin yanzu, Xizang ya zama daya daga cikin yankunan da ke da mafi kyawun yanayin muhalli a duniya. Kokarin da ake ta faman yi a tsakanin gwamnatin tsakiya da ta yankin ya kiyaye wurare masu tarihi na asali da bayar da damar samun ci gaba mai dorewa a karkashin falsafar “ruwan Lucid da tsaunukan lush dukiyoyi ne masu dimbin daraja.”
Bikin cika shekaru 60 na yankin Xizang mai cin gashin kansa ya zarce wata alama ta ci gaba, sai dai a ce wani madubi ne dake nuna yadda yankin ya yi fintikau ta fuskar samun bunkasa daga tsohon yanayinsa na tabarbarewar hanyoyi da rashin habakar tattalin arziki, sakamakon tsare-tsaren da aka yi amfani da su na hangen nesa, da shugabanci na-gari, da kuma karfin ruhin juriya na al’ummarsa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp