Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa (Arewa Coalitions of Youths) ta buƙaci shugaba Tinubu da ya dakatar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, bisa nesanta Shugaban kasa da mataimakinsa da yin maraba da duk wani shirin yaƙin gangamin neman zaɓen shugaban kasa wanda ke tafe nan da 2027.
Ƙungiyar ta yi nuni da cewa, sanarwar da Onanuga ya fitar, za ta iya yin illa ga ruhin ɗimbin magoya bayan tafiyar shugaban kasa da kuma romon dimokuraɗiyya da ake kwankwaɗa a karkashin Gwamnatin Tinubu.
- Cinikin Waje Na Sin Ya Karu Da Kashi 1.3 A Rubu’in Farkon Bana
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Hon. Abubakar Aliyu Galadiman Takai ya rabawa manema labarai a ranar Litinin 14 ga watan Afrilu jim kadan bayan kammala taron kungiyar a ofishinta da ke Kaduna.
“Abin takaici ne cewa, a maimakon yin amfani da gagarumin goyon baya da yunƙurin da ƴan ƙasa ke ginawa, Onanuga ya zaɓi fitar da wata sanarwa mai takurawa. Fahimtar da ya yi wa dokar zabe yana da tsauri fiye da kima kuma ya kasa gane bambanci tsakanin yakin neman zabe ba bisa ka’ida ba da kuma furuci na siyasa na gaske na ‘yan kasa.
“Ƙungiyar gamayyar matasan Arewa ta yi watsi da wannan mataki. Goyon baya ga Shugaba Tinubu na halitta ne kuma a duk faɗin ƙasar, Ginin siyasa ba laifi ba ne.
“Don haka, muna kira da a gaggauta maye gurbin Bayo Onanuga, mai bayar da shawara kan harkokin siyasa da kuma mai bayar da shawara ga kafofin watsa labaru wanda da wanda ya fahimci halin da mutane ke ciki kuma zai iya amfani da dabarar ginin siyasa”. In ji Galadiman Takai.
In ba a manta ba, mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, akwai alluna dauke da hotunan shugaban kasa da na matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, musamman a Abuja da kuma jihar Kano, da ke kama da fara gangamin yakin neman zabe.
A cewar Onanuga, shugaba Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettim na matukar godiya ga dimbin magoya bayansu a fadin kasar nan saboda himima da ci gaba da goyon bayansu, amma shugabannin biyu ba sa goyon bayan duk wani gangamin yakin neman zabe da ya saba wa dokokin kasar nan.
Ya ce, dokar zaɓe da ke jagorantar gudanar da zaɓe da yaƙin neman zaɓe, ta haramta duk wani nau’i na yaƙin neman zaɓe na 2027 a wannan lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp