Tuni dai shirye-shiryen gasar cin kofin duniya ta yi nisa kuma sani wace kasa ce za ta kara da wata a gasar Kofin Duniya na wannan shekarar bayan kammala wasannin neman shiga gasar a Qatar da aka yi a birnin Doha na Qatar.
Gasar wadda za a fara a watan Nuwamba mai zuwa, za ta zama ta farko da za a gudanar a nahiyar Gabas ta Tsakiya kuma ta farko a irin wannan
lokacin na shekara duk da cewa matakin da aka dauka na zabar Katar ya tayar da jijiyoyin wuya.
Za a buga wasannin matakan karshe daga ranar 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Dasamba – lokacin da yanayin zafi ke kai wa 25C a ma’aunin celcius a kasar ta Katar, lamarin da masana suke ganin za’a iya samun tsananin zafi duk da haka.
Da a ce za a buga wasannin a tsakanin Yuni zuwa Yuli, kamar yadda aka saba, za a buga su ne cikin tsananin zafin da ke kai wa fiye da maki 40C, har zuwa maki 50C duk da cewa tun farko Katar ta nemi ta gudanar da gasar a lokacin bazara kuma a rufaffun dakunan wasa masu na’urar sanyaya wuri, amma daga baya sai aka watsar da batun.
Watannin Nuwamba da Disamba cike suke da hada-hada a gasar kasashen Turai ta kungiyoyi kuma ‘yan wasa da yawa za su amsa kira domin buga wa kasashensu wasannin Kofin Duniya a Katar na 2022.
A gefe guda kuma, gasar kasashe kamar Premier League na Ingila, da La Liga ta Sifaniya, da Serie A ta Italiya, za su dakatar da wasanni mako daya kafin fara gasar sai an kammala gasar za su ci gaba da nasu wassannin.
A shekarar 2010 ne Katar ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar ta hanyar lashe zaben da FIFA ta shirya tsakanin mambobinta guda 22. Ta doke kasashen Amurka da Japan da Australia, kuma ita ce kasar Larabawa ta farko da za ta karbi bakuncin gasar.
An zargi Katar da bai wa jami’an tsaro cin hancin Dala miliyan uku da dubu 700 domin samun damar, amma an wanke ta bayan gudanar shekara biyu ana bincike kuma shugaban FIFA na wancan lokacin, Sepp Blatter, ya goyi bayan bukatar Katar a lokacin, amma ya ce da alama FIFA ta yi kuskure.
Yanzu haka Mista Blatter na fuskantar shari’a a kotu a Switzerland bisa zargin zamba da almubazzaranci da sauran tuhumar cin hanci da rashawa tare da abokinsa, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasashen turai, Michael Platini.
Sannan kungiyoyin kare hakki na Amnesty International da Human Rights Watch na zargin Katar da take hakkin ma’aikata ‘yan kasar waje da ke aikin gina filayen wasannin gasar ta cin kofin duniya.
Tun shekara uku da suka gabata aka fara wasannin neman shiga Kofin Duniya kuma kasar Faransa mai rike da kofin a shekara ta 2018, ta tsallake, amma Italiya mai rike da kofin gasar Turai ba ta samu gurbi ba.
A wasannin karshe na cancantar shiga gasar da aka buga, an raba tawagogin kasashe 32 zuwa rukunin tawaga hudu. Tawagogin da suka fito daga nahiya daya an raba su da juna – ban da kasashen Turai, inda ake iya hada kasa biyu a rukuni daya.
Sannan kasashen Brazil da Ingila da Sifaniya na cikin kasashen da ake sa ran za su cinye gasar, kuma ana iya sayen giya ne a manyan otel-otel kawai na Katar, matakin da shima abin dubawa ne musamman ga kasashen da ake shan giya. Katar mai yawan al’umma miliyan 2.9 na daya daga cikin kasashe mafiya arziki a duniya saboda arzikin man fetur da gas da take da su, kuma ta gina sabbin filayen wasa bakwai kawai saboda gasar, da kuma wani sabon birni da za a buga wasan karshe a cikinsa.
Ana gina sabbin otel sama da 100, da sabuwar tashar jirgin kasa da wasu tituna, har ila yau kwamatin shirya gasar ya yi kiyasin cewa ana sa ran mutum miliyan daya da rabi ne za su halarci gasar.
Kamar yadda muka sani kasar Katar ta Musulmi ce mai bin addini sau da kafa saboda haka aka gargadi magoya baya da su kasance masu da’a saboda akwai dokokin hana shan giya kuma ana iya saya ne a manyan otel-otel kawai. Kofi daya na giya kan kai Dala 13 – kwatankwacin Naira dubu biyar, amma kuma masu shirya gasar sun ce za a iya sayar da giyar a wasu kebantattun wurare na ‘yan kallon gasar.
Kungiyoyin kare hakkin ‘yan luwadi da madigo na ta kiran gwamnatocin kasashensu da su tabbatar musu da kariya, yayin da wasu ‘yan kallo daga Wales suka ce za su kaurace wa gasar bayan kasarsu ta samu gurbi.
Masu gasar Kofin Duniyar sun ba da amsa cewa ana maraba da kowa, amma Katar ba za ta sassauta dokokinta ba kan luwadi da madigo, matakin da ake ganin kamar wani tarnaki ne ga kasashen da suka halarta hakan.