An yi hasashen dalar Amurka na iya kaiwa Naira 1,000 a kasuwannin canjin kudin Nijeriya, lamarin dake kara jefa fargabar karuwar tsadar rayuwa a zukatan ’yan Nijeriya. Kwan-gaba-kwan-bayan farashin dalar Amurka a Nijeriya sama da shekara 20 da suka gabata ya dankwafar da darajar Naira.
Majiyoyi daban-daban daga Bankin Duniya sun tabbatar da cewa harkokin shigo da kaya daga waje sun dara na fitar da su yawa a kasar. Na fitarwa wanda da su ake samun dalar, ba su wuce kashi 8.83% ba, na shigarwa kuma kashi 16.57%, sun kusan ninkawa.
Kasashe da dama sun fara farkawa daga baccin rafkana domin yi wa kansu mafita a kan kangin dalar Amurka. Tuni Argentina, Brazil da Bolivia dake nahiyar kudancin Amurka suka fara amfani da kudin kasar Sin, Renminbi a kasuwancinsu da Sin. Abin yana kara samun tagomashi a yankin Latin da Caribbean.
Wajibi ne kasashe su samar wa kansu mafita don rage dogaro da dalar Amurka sakamakon karuwar kudaden ruwa a kan dalar da ramewar asusun ajiyarsu na waje. Masana tattalin arziki na nuna cewa za a samu kasashen duniya da dama da za su rungumi amfani da kudin Sin RMB wajen huldar kasuwanci saboda kasancewar Sin a matsayin kasa mafi girman hada-hadar kasuwanci a duniya. Ko a kwanan baya, an ruwaito shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva yana kiran kasashen duniya su samar wa kansu mafita a kan amfani da dalar Amurka, domin a cewarsa me ya sa dukkan kasashen duniya ke amfani da dalar a kasuwancinsu.
Bugu da kari, gwamnatocin kasashen waje da ke bukatar adana kudaden ajiyarsu na waje da dalar Amurka za su kara kashe kudi wajen neman dalar, inda lamarin zai fi shafar tattalin arzikin kasashe masu tasowa saboda ribar da ake samu wajen fitar da kaya zuwa waje ta ragu.
Haka zalika, Rasha da Sin sun cimma yarjejeniya don fara biyan kudin iskar gas da take samarwa kasar Sin a kudin Yuan da Rubles maimakon Dalar Amurka. Har ila yau, masu sayen man Rasha a Indiya suna biyan galibin kudin mai ne da ko dai kudin Rashar ko kuma Dirham na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Yayin da wannan yunkuri na fita daga kangin dalar Amurka ke samun tagomashi, Kasashe masu kawancen bunkasa ci gabansu na BRICS (Brazil, Rasha, Indiya, Sin, da Afirka ta Kudu) suna shirin kaddamar da sabon kudin da kasashe mambobin kungiyar za su rika amfani da su wajen cinikayya a tsakaninsu. Haka nan gabanin taron kolin kungiyar BRICS na watan Agusta da za a yi a Afirka ta Kudu, yanzu haka akwai kasashe 24 da ke neman kulla kawance domin fita daga tarnakin da dalar Amurka ta yi musu na tsawon shekaru. Kasashen sun hada da Najeriya, Saudi Arabiya, Iran, Argentina, Hadaddiyar Daular Larabawa, Aljeriya, Masar, Bahrain, Indonesia da wasu kasashe na Afirka.
Ko a ’yan watannin baya, Kenya ta sauwake wa kanta nemo Dala Miliyan 500 duk wata don biyan kudin fetur da take shigo da shi, sakamakon kulla yarjejeniya da Kamfanin Mai na Saudiyya (Aramco) da na Abu Dhabi (Adnoc) da za su rika shigo mata da fetur da gas, ita kuma tana biya da kudin kasarta na Shillings.
Ya kamata Nijeriya ta dauki darasi ta farfado da yarjejeniyar musanyar kudin nan a tsakaninta da Sin ta kimanin Naira Biliyan 720 kwatankwacin RMB Biliyan 15 da aka kulla a 2018, saboda kasuwancin dake tsakaninsu wanda ko a watanni ukun farko na shekarar nan ya kai kimanin Naira Tiriliyan Hudu da Biliyan Hamsin da Biyar da Miliyan Dari Biyu da Talatin da Takwas (4,055,238,000.00), kamar yadda aka ruwaito Jami’ar Ofishin Jakadancin Sin a Legas, Ms. Yan Yuqing tana fada a ’yan watannin baya.