Assalamu alaikum mallam, ni AS ce mijina ma ma haka a ‘genotype’, yarana biyu babban yana da AA karamar ‘AS’ duk sanda na sami ciki muna zuwa a duba mana genotype din babyn da ke cikin, likitoci suka tabbatar da SS ne sai musa a cire amma bai kaiwa ‘4months’ muke cirewa, mallam meye hukuncin yin hakan?
Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu. To ‘yar’uwa Malamai sun yi ijma’i a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.
Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta.
Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Sikila ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bauta wa Allah ya amfani al’uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, sai dai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa ba za a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za a tashe shi ranar alkiyama ba.
Allah ne mafi sani.
Macen Da Ba Ta Haila Saboda Tsarin Iyali, Ya Za Ta Yi Idda Idan Aka Sake Ta?
Assalamu alaikum. Malam macen da ba ta haila saboda tsarin iyali ‘family planning’ na wasu watanni, yaya za ta yi idan aka sake ta?
Allah ya kara Ikhlasi.
Wa alaikum assalam. Za ta jira har ta ga jini uku, ko da kuwa za ta yi shekaru (30) kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta yi bayani.
Ina yi wa mata nasiha su nisanci yawancin magunguna da alluran tsarin iyali saboda suna sabbba matsaloli.
Duk da cewa tsarin iyali na wucin gadi ya halatta, sai dai imani da cewa: kowanne abin haihuwa da arzikinsa yake zuwa yana da muhimmanci, saboda hakan zai sa kowa ya samu nutsuwa, ya daina tsorata da yawan yaran da zai haifa.
Allah ne mafi sani.
Mijina Ya Sake Ni Da Danyen Goyo, Yaya Iddata?
Assalamu Alaikum, Dr. Tambaya ce: Mace mijinta ya sake ta bayan ta haihu da danyen goyo, ya iddarta za ta kasance? Allah ya kara wa Dr. Ikhlasi.
Wa alaikum assalam. Za ta jira jini uku kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta yi aure ba har sai ta kammala su.
Allah ya kara mana ikhlasi a duka lamuranmu.
Allah ne mafi sani.