• Leadership Hausa
Thursday, August 18, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Taskira

Ya Halatta Mu Zubar Da Ciki Ni Da Mijina Idan Likita Ya Gaya Mana Yaron Da Za Mu Haifa Sikila Ne? (Fatawa)

by Dakta Jamil Zarewa
2 months ago
in Taskira
0
Ya Halatta Mu Zubar Da Ciki Ni Da Mijina Idan Likita Ya Gaya Mana Yaron Da Za Mu Haifa Sikila Ne? (Fatawa)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Assalamu alaikum mallam, ni AS ce mijina ma ma haka a ‘genotype’, yarana biyu babban yana da AA karamar ‘AS’ duk sanda na sami ciki muna zuwa a duba mana genotype din babyn da ke cikin, likitoci suka tabbatar da SS ne sai musa a cire amma bai kaiwa ‘4months’ muke cirewa, mallam meye hukuncin yin hakan?

Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu. To ‘yar’uwa Malamai sun yi ijma’i a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta.

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Sikila ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bauta wa Allah ya amfani al’uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, sai dai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa ba za a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za a tashe shi ranar alkiyama ba.
Allah ne mafi sani.

Macen Da Ba Ta Haila Saboda Tsarin Iyali, Ya Za Ta Yi Idda Idan Aka Sake Ta?

Labarai Masu Nasaba

Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye Ne, Saurayi Ko Budurwa?

Salon Zance Tsakanin Saurayi Da Budurwa A Zamanin Nan

Assalamu alaikum. Malam macen da ba ta haila saboda tsarin iyali ‘family planning’ na wasu watanni, yaya za ta yi idan aka sake ta?
Allah ya kara Ikhlasi.
Wa alaikum assalam. Za ta jira har ta ga jini uku, ko da kuwa za ta yi shekaru (30) kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta yi bayani.
Ina yi wa mata nasiha su nisanci yawancin magunguna da alluran tsarin iyali saboda suna sabbba matsaloli.
Duk da cewa tsarin iyali na wucin gadi ya halatta, sai dai imani da cewa: kowanne abin haihuwa da arzikinsa yake zuwa yana da muhimmanci, saboda hakan zai sa kowa ya samu nutsuwa, ya daina tsorata da yawan yaran da zai haifa.
Allah ne mafi sani.

Mijina Ya Sake Ni Da Danyen Goyo, Yaya Iddata?

Assalamu Alaikum, Dr. Tambaya ce: Mace mijinta ya sake ta bayan ta haihu da danyen goyo, ya iddarta za ta kasance? Allah ya kara wa Dr. Ikhlasi.
Wa alaikum assalam. Za ta jira jini uku kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta yi aure ba har sai ta kammala su.
Allah ya kara mana ikhlasi a duka lamuranmu.
Allah ne mafi sani.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Amfanin Manhajar Gmail A Wayoyin Hannu

Next Post

Brazil Ta Ci Gaba Da Zama Ta Daya A Duniya

Related

Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye Ne, Saurayi Ko Budurwa?
Taskira

Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye Ne, Saurayi Ko Budurwa?

5 days ago
Salon Zance Tsakanin Saurayi Da Budurwa A Zamanin Nan
Taskira

Salon Zance Tsakanin Saurayi Da Budurwa A Zamanin Nan

2 weeks ago
Bukukuwan Babbar Sallah: Wane Tanadi Matasa Suka Yi?
Taskira

Bukukuwan Babbar Sallah: Wane Tanadi Matasa Suka Yi?

1 month ago
Rashin Yaba Kwalliyar Mace Daga Mijinta: A Ina Gizo Yake Sakar?
Taskira

Rashin Yaba Kwalliyar Mace Daga Mijinta: A Ina Gizo Yake Sakar?

2 months ago
Kishi Kumallan Mata
Taskira

Kishi Kumallan Mata

2 months ago
Matar Wani
Taskira

Matar Wani

2 months ago
Next Post
Brazil Ta Ci Gaba Da Zama Ta Daya A Duniya

Brazil Ta Ci Gaba Da Zama Ta Daya A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Fada Ya Barke Tsakanin Shugabannin ’Yan Bindiga, 2 Sun Mutu Yayin Rikicin A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Shingen Bincike Na ‘Yan Sanda Sun Harbe Mutum 2 A Ebonyi

August 18, 2022
An Cafke Mutumin Da Zai Aike Da Bindigu Kano Daga Abuja Ta Tashar Mota

An Cafke Mutumin Da Zai Aike Da Bindigu Kano Daga Abuja Ta Tashar Mota

August 18, 2022
Neman ‘Yancin Nijeriya: Dr Nnamdi Azikiwe da Ahmed Mahmud Saad Zungur A Landan.

Ku Yi Watsi Da Masu Wa’azin Son Wargaza Hadin Kan Nijeriya —IBB

August 18, 2022
Kungiyar Haɗin Kan Musulunci ta Duniya Ta Ziyarci Medina Baye Niass

Kungiyar Haɗin Kan Musulunci ta Duniya Ta Ziyarci Medina Baye Niass

August 18, 2022
Neman ‘Yancin Nijeriya: Dr Nnamdi Azikiwe da Ahmed Mahmud Saad Zungur A Landan.

Neman ‘Yancin Nijeriya: Dr Nnamdi Azikiwe da Ahmed Mahmud Saad Zungur A Landan.

August 18, 2022
Majalisar Jihar Zamfara Ta Zartar Da Dokar Kariya Ga Masu Bukata Ta Musanman

Matawalle Ya Amince Da Hukuncin Kisa Kan Masu Garkuwa Da Masu Ba ‘Yan Bindiga Bayanan Sirri

August 17, 2022

Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Janye Yajin Aikin Da Suka Fara Na Mako 2

August 17, 2022
Kudin Shigar Manyan Kamfanonin Kera Na’urorin Sadarwa Na Sin Ya Kai Yuan Triliyan 14 A 2021

Kudin Shigar Manyan Kamfanonin Kera Na’urorin Sadarwa Na Sin Ya Kai Yuan Triliyan 14 A 2021

August 17, 2022
Yanayin Kare Hakkin Dan Adam Na ‘Yan Kananan Kabilun Sin Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

Yanayin Kare Hakkin Dan Adam Na ‘Yan Kananan Kabilun Sin Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

August 17, 2022
Gaskiya Ba Ta Buya…

Gaskiya Ba Ta Buya…

August 17, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.