Shugaba Muhammadu Buhari wanda kuma zakaran yaki da rashawa ne a Afrika, a ranar Alhamis ya yi kira da aka kafa Kotun kasa da kasa na hukunta wadanda aka kama da aikata rashawa, inda ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da su kara himma wajen yaki da cin hanci da rashawa tare da kara samar da yanayin kiyaye dukiyoyin al’umma.Â
A jawabinsa da aka nada da ya yi na bikin ranar yaki da rashawa ta Afirka, kamar yadda sanarwar da Kakakin Shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya kuma nemi shugabannin kasashen Afirka da su kara azama wajen gurfanar da wadanda aka kama da hannu a aikata rashawa domin hakan ya zama izina ga na baya.
Buhari ya ce, rashawa na matukar ruguza kasashen Afirka don haka ne ya nemi su hada karfi da karfe su tunkari rashawa domin tabbatar da cigaba mai daurewa.
“A Nijeriya tun 2015 muke yaki da cin hanci da rashawa, kuma an cimma nasarori masu yawa na kamawa da gurfanar da wadanda ake zargi tare da daure wadanda aka kama da aikata rashawa tare kuma da kwato kadarorinsa dama bisa dokokin da suka shafi yaki da rashawa da cin hanci.”
Ya ce samar da kotun hukunta masu cin hanci da rashawa ta duniya zai taimaka sosai wajen rage kaifin handame dukiyar al’umma tare da yin babakere a kai. Ya kuma bukaci a kafa karfi wa hukumomin da suke yaki da cin hanci da rashawa tare da basu dukkanin goyon bayan da suka kamata domin su cigaba da yaki da masu aikata laifuka rashawa a cikin al’umma.