Daya daga cikin ‘ya’yan wakilin LEADERSHIP Hausa na Jihar Filato, Lawal Umar Tilde mai suna Usman Lawal ya yi batan dabo, inda aka nemi shi ko kasa ko sama amma ba a same shi ba.
Usman Lawal wanda dalibi ne a Makarantar kwana ta gwamnati ta ‘Senior Secondary School Toro’, da ake kira T C.Toro, a Jihar Bauchi ya bar gidan mahaifansa ne da ke Unguwar Kawohi kusa da Asibitin Usmaniyya, a garin Tilden Fulani ranar Jumma’ar makon da ya gabata, jim kadan bayan dawowarsa gida daga hutun babbar Sallah da makarantarsu ta bayar.
Usman dan shekara 16 da haihuwa sau da yawa yana fada wa kannensa cewa zai je ya yi hutun Babbar Sallah a gidan abokinsa a garin Bauchi. Ya bar gida da misalin karfe daya da mintin ashirin na rana yana amsa waya.
Mahaifin Usman, yana rokon duk wanda Allah ya sa ya gan shi ya kai ma ‘yansanda ko shugabannin addini rahoton hakan, bugu da kari kuma ya bar gida yana cikin saye da kayan makarantarsu.