Jama’a, idan kun ziyarci Gidan Tunawa Da Kisan Kiyashin Nanjing da ke birnin Nanjing na kasar Sin, za ku ga mutum-mutumin wata uwa tana kuka, wadda ke rike da danta da aka kashe, kuma tana kallon sama don bayyana matukar bacin ranta. Wannan shi ne misalin ta’asar da Japanawa suka aikata a Nanjing daga ranar 13 ga Disamban 1937 zuwa Janairun 1938, cikin makonni shida kawai, sama da Sinawa 300,000 sun halaka sakamakon kisan kiyashin da maharan Japan suka yi musu.
Daga 1931 zuwa 1945, al’ummar kasar Sin sun kwashe shekaru 14 suna yakin kin maharan Japan, kuma a karshe sun ci nasara. A cikin wadannan shekaru, Sinawa kimanin miliyan 35 sun rasa rayukansu, ciki har da sojoji miliyan 3.8 da fararen hula miliyan 20. Don haka, kasar Sin ta yi babbar sadaukarwa a yakin kin harin mulkin danniya a duniya, kuma ba shakka yakin da Sin ta yi da maharan Japan ya kasance wani muhimmin bangare na yakin.
Al’ummar duniya sun sha yin Allah-wadai da kisan kiyashin da Jamus ta yi wa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu. Kuma Jamus ta yi nadamar laifukanta a bainar jama’a.
Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi, a yunkurin gujewa hukunci da al’ummar duniya za su yi musu.
Mace macen da aka samu a yakin duniya na 2, abun bakin ciki ne ga dukan bil’adama. Al’ummomin kasashen duniya suna da makoma da tarihi na bai daya, wanda ba za a iya mantawa da shi ba, balle a gyara shi.
A bana ake cika shekaru 80 da nasarar yakin kin harin mulkin danniya a duniya, da kuma nasarar da kasar Sin ta cimma ta yakar maharan Japan. A wannan muhimmin lokaci na tarihi, ra’ayin da ake dauka kan tarihin ya zama ma’aunin kimanta mutuncin bil’adama da kuma ma’aunin kiyaye tsarin duniya bayan yakin. Mu yi kokarin kiyaye sahihin tarihin yakin ba don tunawa da mamata ba ne kawai, amma don daukar alhakin da ya rataya a wuyanmu.(Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp