Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fada a baya-bayan nan cewa, zai gana da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, a yayin taron kolin kungiyar G20, inda mai yiwuwa su tattauna kan batutuwa masu tada kura, kamar batutuwan da suka shafi Taiwan da sauran su.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis 10 ga wata cewa, bangaren kasar Sin yana mai da hankali sosai kan shawarar da bangaren Amurka ya bayar, ta gudanar da tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, kuma a halin yanzu bangarorin biyu suna mu’amala kan wannan batu.
A cewarsa, ya kamata bangaren Amurka ya hada gwiwa da kasar Sin, don tinkarar bambance-bambance yadda ya kamata, da inganta hadin gwiwa irin na samun moriyar juna, da kaucewa rashin fahimta, ta yadda za a dora dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta dace ta samun ci gaba yadda ya kamata.
Baya ga haka, kakakin ya jaddada cewa, batun Taiwan jigon moriyar kasar Sin ne, kuma abun da ya kamata Amurka ta yi shi ne, ta daina yin karya, da ruguzawa, da murkushe manufar Sin daya tak a duniya.
Kana ta kiyaye ka’idojin huldar kasa da kasa, na mutunta mulkin kai da cikakken yankin kasa, da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, da komawa kan sanarwoyin nan uku, da Sin da Amurka suka amince da su bisa hadin gwiwa, da manufar kasancewar Sin daya tak a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)