• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Amurka Ta Sauya Mahangar Ta Game Da Sin

by CMG Hausa
3 years ago

Ga duk mai bibiyar kalaman wasu ’yan siyasar Amurka, ba zai rasa jin kalamai dake bayyana kasar Sin a matsayin abokiyar hamayya ko taraka da ya wajaba Amurka ta takawa birki ba.

A daya hannun kuwa, kasar Sin ta sha bayyana wannan mahanga ta Amurka a matsayin kuskure, tare da nanata kira ga Amurka da ta rika kallon alakar dake tsakanin kasashen biyu sama da batun takara kadai, domin kuwa a matsayinsu na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, Sin da Amurka na iya gudanar da hadin gwiwa da cudanya mai tsafta, ba tare da shiga takun saka ko fito na fito ba.

  • Kasar Sin Na Samar Da Agajin Jin Kai Ga Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa A Syria

Karkashin matakan da Amurka ke dauka, na bayyana adawa a zahiri ga Sin, an ga yadda take yin matsin lamba ga halastattun hakkokin wasu kamfanonin Sin, tare da kakkaba musu takunkumai, inda a wasu lokutan hakan kan kawo tsaiko ga tsarin samar da hajojin masana’antu na duniya.

Ko da yake shugabannin Amurka a wasu lokacin kan ce ba su da nufin haifar da tashin hankali tsakaninsu da bangaren Sin, amma matakai na zahiri da suke dauka na sabawa hakan, musamman duba da cewa, har kullum Amurka tana jaddada aniyar nan ta “Sanya bukatu da muradun kasar gaban komai”, ba tare da la’akari da bukatar wanzar da daidaito da lura da bukatun sauran sassan duniya ba.

Ko shakka babu duniya na da fadin da kasashen biyu za su iya aiwatar da dukkanin matakan raya kansu yadda ya kamata, ba tare da sun hari juna, ko sun shiga cacar baka maras amfani ba. Kazalika wanzar da kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Amurka, zai kare moriyar al’ummunsu baki daya, tare da burikan da sauran sassan kasa da kasa suke fatan ganin an cimma.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Yayin da kasar Sin ke ta kokarin ganin ta inganta alakarta da Amurka, karkashin manufofin martaba juna, da kaucewa mummunar takara, da zama da juna lami lafiya, da gudanar da hadin gwiwa don cimma moriya tare, ya kamata a nata bangare ita ma Amurka ta yi watsi da ra’ayin nan na “Ko na samu ko kowa ya rasa”.

Bugu da kari, dukkanin wata nasara da kasashen 2 za su samu, za su kasance damammaki na bunkasar dukkanin sassan duniya, don haka ya zama wajibi Amurka ta sauya mahangarta game da Sin, ta kalli Sin a matsayin abokiyar cudanya da za a yi tarayya da ita wajen wanzar da ci gaba mai ma’ana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Dan Takarar Gwamnan ZLP A Bauchi Ya Musanta Janye Takararsa

Dan Takarar Gwamnan ZLP A Bauchi Ya Musanta Janye Takararsa

LABARAI MASU NASABA

Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.