• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Amurka Ta Soke Takunkumi Idan Tana Son Taimakawa Afirka

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Ranar 25 ga wata, rana ce ta yaki da takunkumi, wadda kungiyar SADC ta ayyana. Wasu kasashen Afirka sun sake yin kira ga Amurka da sauran kasashen yammacin duniya da su soke takunkumin da suke kakabawa kasar Zimbabwe.

Amurka ta dauki sama da shekaru 20 da sanyawa Zimbabwe takunkumi ya zuwa yanzu. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, Zimbabwe ta yi asarar dalar Amurka fiye da biliyan 40 sakamakon takunkumin da aka sanya mata baki daya.

  • Xi Jinping Ya Taya Murnar Kafuwar Cibiyar Kasa Da Kasa Ta Bunkasa Kirkire-Kirkire Da Ilimi Domin Wanzar Da Ci Gaba A Fannin Sufuri

Hakika dai yadda Amurka ta kakabawa Zimbabwe takunkumi, ta nuna yadda ta dade tana tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen Afirka.

A watan Agustan bana, Antony Blinken, sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci Afirka karo na 2, inda ya gabatar da sabbin tsare-tsaren Amurka kan yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Amurka ta yi shelar cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, za ta kara azama kan yadda Afirka take bude kofa ga ketare, da taimakawa Afirka wajen tinkarar annobar cutar COVID-19 da farfado da tattalin arzikin Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Amma akasarin ra’ayoyin jama’a na ganin cewa, a maimakon taimakawa ci gaban Afirka, Amurka ta yi amfani da Afirka domin samun moriya bisa manyan tsare-tsare, da sunan wai hada kai da Afirka.

Yanzu haka sakamakon tsanantar rikicin Ukraine, ya haifar da karuwar barazanar karancin abinci da makamashi, lamarin da ya kawo wa kasashen Afirka wadanda ke neman farfado da tattalin arzikinsu babban kalubale.

Duk da haka Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun kau da kai daga matsalar da Afirka ke fuskanta wajen samun ci gaba, sun ci gaba da kara sanya takunkumi kan kasashe masu ruwa da tsaki, har ma sun tilasta wa kasashen Afirka ba su goyon baya.

Ko Amurka tana son taimakawa Afirka, ko kuma ba za ta cika alkawarinta kamar yadda ta yi a baya? Gaskiya ba ta buya. Kafin Amurka ta hada kai da Afirka, ya kamata ta soke takunkumin da take kakabawa wasu kasashen nahiyar.(Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Kusan Mutane Biliyan 1.03 Na Da Inshorar Tsoffi A Kasar Sin

Kusan Mutane Biliyan 1.03 Na Da Inshorar Tsoffi A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.