Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa da ke yankin Kudancin Nijeriya a Jihar Legas, ta yi kira ga shugaban Hukumar Yaki da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Buba Marwa ya mike haikan wajen yaki da bata-garin ‘yan siyasa da ke raba kwayoyi ga matasa don ingiza su bangar siyasa.
A cewar gamayyar, bata-garin ‘yan siyasar suna amfani da kwaya wajen jirkita tunanin matasa don su cimma muradunsu na son zuciya.
Shugaban Gamayyar Matasan, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanchi, wanda ya yi kiran a zantawarsa da manema labarai, ya kara da cewa, “Tun da yanzu an shiga lokacin siyasa gadan-gadan, bata-garin ‘yan siyasa suna nan babu abin da suke yi illa sayen miyagun kwayoyi suna raba wa matasa.
Don haka muke kira ga ga Shugaban NDLEA, Buba Marwa ya kara mikewa tsaye wajen sa ido a kan yadda wadannan bata-garin ‘yan siyasar suke amfani da kwaya su lalata tunanin matasa, su ingiza su cikin bangar siyasa don cimma burinsu.”
Wakazalika, gamayyar ta yi kira ga wakilan al’umma a majalisun dokoki a matakai daban-daban su kafa wata doka da za ta hana bangar siyasa, “Kuma muna kira ga sanatoci da ‘yan majalisar dokoki su ji tsoron Allah su yi dokar da za ta hana bangar siyasa domin ceton matasa.
Don babu ‘yan siyar da suke daukar ‘ya’yansu su je da su wajen taron siyasa domin gudun abin da zai je ya dawo. Wannan shi ne rokon da muke yi a gare su, domin amana ce suka dauka kuma Allah ba zai bar su ba sannan muna sake kira ga shugabanni musamman wadanda suka fito daka arewacin kasarmu su ji tsoron haduwarsu da Allah, domin sun san yadda yankinsu yake ciki, amma sun gaza yin abin da ya dace.”
Gamayyar ta kara da cewa, hatta su kansu ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ta APC sun san ba a yi abubuwan da suka kamata wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar nan ba.
“Mun dade muna gaya wa wakilanmu da sauran shugabanninmu na arewa cewa ba a yin abubuwan da suka kamata wajen magance matsalar nan ta kashe-kashen jama’a. Ga shi yanzu hatta su kansu wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa na APC sun yi tsokaci a kan kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake yi wanda gwamnati ba ta yi abin da ya dace ta yi ba na kawo karshen wadannan masifun. Mun tabbatar da cewa mutum daya ba zai iya ba dole sai an hada karfi da karfe.
“Dan haka muke kara kai kukanmu ga Ubangiji da ya ba mu shugabanni nagari wadanda za su hana yi mana kisan gillah kuma muna kira da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ta yi dokar hana deligate a siyasar Nijeriya kafin ta sauka domin wannanma zai taimaka wa alumma.
“Haka nan muna kara kiga ga matasa su kula saboda sun ga yadda tsarin siyasarmu yake, ba a kulawa da su sai in za a saka su bangar siyasa a ba su kwaya.” In ji shi.